10 Oktoba 2021 - 16:39
Ana Zaben ‘Yan Majalisar Dokoki A Iraki

A Iraki, yau ne al’ummar kasar da suka cancanci zabe ke kada kuri’a a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : An kiyasta masu zabe kimanin miliyan 25 ne zasu kada kuri’a a zaben na gabanin wa’adi, domin sabunda ‘yan majalisar dokokin kasar.

Zaben, an kira shi ne da zumar biyan bukatun masu boren da ya barke a watan Oktoban 2019.

Masu zanga zangar a waccen lokacin wandanda mafi akasarinsu matasa ne sun koka ne kan matsalar cin hanci da rashawa da rashin aikin yi.

Kafin hakan dai rahotanni sun ce an tsaurara matakan tsaro a sassa daban daban na kasar, domin baiwa jama’a damar kada kuri’a cikin tsanaki.

342/